JAMB - Hausa (2019)

1
'Baba na cin abinci yanzu'. Kalmar suna a wannan jimla ita ce
Answer
(B)
Baba
2

PASSAGE 2: Damukowa mutum ne wanda irin halayensa ne suka sa ake kiransa da wannan suna. Domin yana da kinibibi, da gulma, da ketti da rashin mutunci da rashin ganin kimar kowa. Kuma yana kiwon dabbobi kamar jakai da rakuma da rakuma da tumakai da kaji har da shanu. Asalin garin Damukowa shi ne Gunu wanda idan za a je garin sai an keta dazuzzuka da rafuka, kuma ana cin karo da dabbobin da kamar birai da kuraye da macizai da giwaye amma babu damisa da zaki. Idan damina ta sauka Mai unguwar Gunu kan umurci jama'a da su d'aure dabbobinsu don kar su yi barnar amfanin gonarsu kamar masara da dawa da gyada da wake amma ban da auduga domin ba sa nom ta. Nan ne fa Damukowa kan nuna halayensa na rashin ga umurnin Mai unguwa na kin daure dabbobinsa. Idan dabbobinsa sun yi barna a gonakin mutane yakan bijire wa dogaran da suka zo kama shi har ya sa a yi musu duka du keta musu tufafi, har ma da ji musu ciwo. Garin Gunu na makwabtaka da Shakwatu da Gwada da Badum da Akope. Cikin mutanen wadannan garuruwa akwai maharba da masunta da makiyaya da manoma amma babu madora.

Duk wadannan halayen Damukowa ne in ban da

Answer
(D)
barna
3

(Almost identical passage as above, with minor differences at the end)

...Damukowa yana kiwon wadannan dabbobi in ban da.

Answer
(B)
macizai
4

(Again similar passage)

Wahe abu ne mutanen garin Gunu ba su nomawa?

Answer
(A)
Auduga
5

(Again similar passage)

Ware bare.

Answer
(C)
Madora
6

INSHA'I

Ana warware kunshin jawabi ne a

Answer
(C)
kammalawa
7
A rubutun wasika daga adireshi sai
Answer
(B)
adireshi na biyu
8
'Malam ya sayi mota shud'iya jiya'. Fito da sifa daga wannan jimlar.
Answer
(D)
Shud'iya
9
Wace jimla ce ba ta d'auke da sifa?
Answer
(D)
Nan-nan ya kasa kai damin dawa
10
Wakilin suna na biyu, mace kuma tilo ita ce
Answer
(C)
ita
11
A gundarin jawabi ne aka fi amfani da wadannan in ban da
Answer
(A)
kwanan wata
12
Ana amfani da d'afin - una wajen jam'in duk wadannan in ban da
Answer
(A)
rafi
13
'Sa hannun mai rubutu' yana zuwa ne a
Answer
(C)
kasa daga dama
14
Bayanau a nahawu na nufin kalmar da ke Karin bayani a kan
Answer
(A)
aikatau
15
Insha'in da ake 'bugun jaki, sanman a bugi taiki da hujjoji shi ne na
Answer
(D)
muhawara
16
Wace ce ta yi tafiya jiya Wannan jimlar......... ce
Answer
(A)
Karfafawa
17
Gano jimla korau a wad'annan.
Answer
(B)
Kar ka zo gobe
18
Damukowa ya fito daga
Answer
(B)
Gunu
19
Ware bare dangane da jam'i a tambaya ta 32 da ta 33.
Answer
(D)
Littafi
20
NAHAWU Fati ta ga akuya wadda ta shanye ruwa." Wannan jimla ......ce.
Answer
(D)
sassauka
21
Fito da wakilin suna na uku kuma jam'i.
Answer
(B)
Su
22

AUNA FAHIMTA Karanta wadannan labarai, sannan ka amsa tambayoyin da ke biye. Idan mutum ya kama sana'a, musamman a cikin sana'o'in Hausa na gargajiya tamkar ya shiga wani kulob ne. Dalili kuwa, kowace sana'ar Hausa ta gargajiya za ka iske tana da wadansu al'adu nata daban. Misali an san Mahauta a kan al'adar hawan kaho, da kuma iya mayar da magana. Sa'annan an san Makera da wasan cin-wuta, su ko Maharba kan bayar da magunguna irin na saiwa da sassake-sassake, da sauransu. Wasu sana'o'in har unguwanni gare su a cikin birane. Saboda haka idan bakon mai sana'a ya shigo gari, yakan nemi unguwar masu sana'a irin tasa ne, ya je ya zauna. Zaman irin wannan unguwar zama ne na cude-ni-in-cude-ka wajen aiki, ko a fagen kayan aiki, ko wajen dabarun samun kasuwa, da sauransu. Sa'annan dukkar sana'o'i suna da sorakuna, masu kula da zamansu a gari. Kuma su ne tsani daga masu sana'a zuwa ga hukumar gari ko kasa. Misali akwai Sarkin gini, da Galadiman gini, da Madakin gini, da Wakilin gini, da Sarkin fawa, da Wakilin fawa, da Sarkin aska, da Dangaladima, da Sarkin Makera, da sauran irinsu.

...it...i...i...i...i...i...i...i...i...i...i...i...i...

Answer
(C)
Mahauta
23

(same passage as above, slightly extended at the end)

Sana'o'in Hausa na gargajiya sun kunshi wadannan al'adu in ban da

Answer
(D)
zaman unguwa.
24

(same passage)

Sarkin fawa shi ne mai kula da

Answer
(A)
Mahauta
25

(same passage)

Ware bare dangane da masu sarautar gini

Answer
(D)
Dangaladima
26

(same passage, extended)

Tamkar ya shiga wani kulob ne'. Kalmar da aka ja wa layi na nufin

Answer
(B)
kungiya
27
Wace jimla ce ba ta d'auke da sifa?
Answer
(C)
Akuya na kuka ainun.
28
Da malalaci da mayaudari duk malalaciya ce uwarsu. Kalmomin sifa nawa ne a cikin wannan jimla?
Answer
(A)
Uku
29
Wakili ya auri wata farar yariniya." Kalmar da aka ja wa layi........ce.
Answer
(B)
aikatau
30
'Audu ya fadi a rigingine'. Bayanau a nan shi ne
Answer
(B)
a rigingine
31
Tsamo kalmar wakilin suna mutum na biyu namiji kurma tilo
Answer
(A)
Shi
32
Ware bare dangane da sunayen yanka.
Answer
(C)
Balarabe
33
Wanne ne ba sunan yanka ba?
Answer
(C)
Gambo
34
"Awakai sun fita gida da gudu." Kalmar aikatau a wannan jimla ita ce
Answer
(C)
fita
35
Gano kalmar bayanau.
Answer
(B)
Yi