JAMB - Hausa (2022 - No. 34)

Ambaliyar ruwan ke da wuya, sai ta yi awon gaba da wasu gadaje da katifu da akwatuna har ma da asabari. Amma ban da burgami da
gafaka da zabirar Tanko, saboda suna rataye a sama. Sai kuma turmi da randunan matarsa su ma kuwa nauyinsu ne ya hana ruwa ya yi
awon gaba da su. Haka kuma dawarsa da geronsa na kulle ne a rumbu, wannan shi ne dalilin da ya hana ruwa awon gaba da su. Har ila yau
Tanko ya kuma tsira da dawaki da shanu da tumaki da agwagi saboda sun iya ruwa, baka zalika ya tsira da darninsa domin ya yi masa kafi
mai kyau. Amma makwabcinsa Jikan Dara ya yi hasara matuka, saboda ruwa ya yi awon gaba da jakunansa kakaf, domin su ba gwanayen
iya ruwa ba ne. Yanzu haka idan ka je Zuguru, za ka tarar da jamaʼa kungiya-kungiya suna tururuwa zuwa gidan Tanko don yi masa jaje,
saboda kirkinsa da taimakon da yake yi wa jama'a. Amma makwabcinsa Jikan Dara sai tir jama'a ke yi masa, musamman Bala da 'Dan'
umma da 'Dantata domin su tsararrakinsa ne, sun kuma fi kowa sanin rashin kirkinsa ..
Burgami da gafaka da zabira sun tsira daga ambaliya saboda.
iya ruwansu
Kafi mai kyau
suna kulle a rumbu
Babu ko ɗaya daga cikin waɗannan

Comments (0)

Advertisement