JAMB - Hausa (2021 - No. 33)
AUNA FAHIMTA
Karantar wadannan labarai, sannan ka amsa tambayoyin da ke biye da su.
Hausawa sukan sami suna daga lokaci ko hali korana ko yanayi ko faruwar wani abu. Alalmisali,idan aka haifi yaro a wani lokaci kamar, dare sai akira shi 'Dandare, in kuwa da hantsi ne sai akira shi 'Nahantsi ko Magawata idan an haife shi a farkon wata. ko Ciwake idan lokacin ana cin wake, ko Damina idan ana ruwan sama.
Idan kuwa aka haifi yaro a wata rana sai a ba shi Suna da irin wannnan ranar; kamar Danliti ko Attine,ko Tanimu ga wanda aka haifa ran Litinin, idan kuwa Talata ce akan kira yaro da suna Dantala,ko Taku ko Lantana ko Talatu. Haka kuma Laraba ko Larai. Alhamis kuwa Lam ko Danlami.
Najuma ko Danjuma da Juma ko Jummai suney'an Juma'a. Dan Asabe ko Asabe ko Assibi ko Subdu su ne aka haifa ran Asabar.
Akwai kuma sunayen da ake sa wa yaro dangane da halayyar da aka haife shi a ciki. Misali: Talle wanda uwarsa ta mutu lokacin haihuwa ko Audi wanda ubansa ya mutu yana ciki. Idan kuwa aka haifi namiji bayan 'ya'ya mata uku ko fiye shi ne Mato, ko Delu ko Kande ko ko Dela wadda ta biyo maza da yawa. Gambo kuwa wanda aka haifa bayan tagwaye.Duk wadannan sunayen lokaci ne in ban da
Explanation
Comments (0)


