JAMB - Hausa (2018 - No. 15)

PASSAGE 2: Ambaliyar ruwan ke da wuya, sai ta yi awon gaba da wasu gadaje da katifu da akwatuna har ma da asabari. Amma ban da
burgami da gafaka da zabirar Tanko, saboda suna rataye a sama. Sai kuma turmi da randunan matarsa su ma kuwa nauyinsu ne ya hana
ruwa ya yi awon gaba da su. Haka kuma dawarsa da geronsa na kulle ne a rumbu, wannan shi ne dalilin da ya hana ruwa awon gaba da su.
Har ila yau, Tanko ya kuma tsira da dawaki da shanu da tumaki da agwagi saboda sun iya ruwa, baka zalika ya tsira da darninsa domin ya
yi masa kafi mai kyau. Amma makwabcinsa Jikan Dara ya yi hasara matuka, saboda ruwa ya yi awon gaba da jakunansa kakaf, domin su b;
gwanayen iya ruwa ba ne. Yanzu haka idan ka je Zuguru, za ka tarar da jamaʼa kungiya-kungiya suna tururuwa zuwa gidan Tanko don yi
masa jaje, saboda kirkinsa da taimakon da yake yi wa jamaʼa. Amma makwabcinsa Jikan Dara sai tir jama'a ke yi masa, musamman Bala d
'Dan' umma da 'Dantata domin su tsararrakinsa ne, sun kuma fi kowa sanin rashin kirkinsa.
Burgami da gafaka da zabira sun tsira daga ambaliya saboda.
suna rataye a sama.
Kafi mai kyau
iya ruwansu
nauyinsu

Explanation

Burgami da gafaka da zabira sun tsira daga ambaliya saboda ... (Burgami, gafaka, and zabira were saved from the flood because ... ). Answer:
suna rataye a sama (they were hanging above)
The passage states that burgami, gafaka, and zabira were saved from the flood because they were hanging above, out of reach of the water

Comments (0)

Advertisement